Kimanin mutane 15 ne aka kama a yankin Aguleri da ke karamar hukumar Anambra ta Gabas, mahaifar tsohon gwamna, Cif Willie Obiano.
Kamen ya biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin ‘yan kungiyar asiri da jami’an ‘yan sanda a yankin.
Wata majiya ta ce wasu ‘yan bindiga dauke da bindigu ne suka mamaye al’ummar garin da misalin karfe 11 na safiyar Lahadi inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi, lamarin da ya sa mazauna garin suka tsere.
Ana zargin ‘yan bindigar ‘yan kungiyar asiri ne da ke fafatawa da wata kungiyar da ke hamayya da juna. Jami’an ‘yan sanda ne suka shiga tare da yi musu artabu da bindiga.
Wata majiya ta ce ba a samu asarar rai ba amma mutane da dama sun samu raunuka daban-daban sakamakon harbin.
Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, Ikenga Tochukwu ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai ya musanta ikirarin cewa ‘yan sanda sun jikkata, ya kara da cewa an kama wasu daga cikin ‘yan kungiyar asiri.
A cewar PPRO: “An shawo kan lamarin, bisa umarnin kwamishinan ‘yan sanda, Echeng Echeng. Mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka ya jagoranci jami’an ‘yan sanda zuwa wurin tare da hana matasan farmaki ofishin ‘yan sanda.”
Ya tabbatar da cewa an kama sama da mutane 15 yayin da aka kwato wasu muggan makamai.
Ya kuma tabbatar da cewa, ‘yan sanda na lalubo hanyoyin warware rikicin, ciki har da yin kira da a yi sulhu a tsakanin matasan da suka fusata.
“Mun kuma tsananta sintiri a yankin, da nufin inganta zaman lafiya da tsaro,” in ji shi.