Jami’an tsaro sun kama mutum 14 dauke da miliyoyin naira da ake zargin suna amfani da kudaden wurin sayar da sabbin kudi a birnin Kano da ke arewacin kasar.
Da yake magana da manema labarai yayin gabatar da wadanda ake zargin, Kwamandan jami’an tsaro ta NSCDC a Kano, Adamu Zakari, ya ce an kama su ne a kwaryar birnin suna cinikin sabbin kudin.
Ya ce sana’ar tasu ta ci karo da dokar Babban Bankin Najeriya CBN sashe na 20, wanda ya hana sayar da kudi.
A gaban manema labaran wasu daga cikin wadanda aka kama din sun ce neman na abinci ne ya sa suke sana’ar.
Sashe na 20 na kundin dokar Babban Bankin Najeriya ya haramta yin jabun kudi, ko talla, ko kuma sayar da takardar kudin naira, ko kuma duk wani kudi da ke fita daga bankin.