fidelitybank

An kama mutane 13 ciki harda sojoji 4 da zargin fashi a Ribas

Date:

Rundunar ‘yansanda reshen jihar Ribas, ta kama mutum 13 da zargin fashi da makami, da satar kayan abinci.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta fitar ta ce cikin waɗanda ake zargin akwai soja huɗu, da ɗan rundunar tsaro ta Civil Defence.

Grace Iringe-Koko ta ce sun yi nasarar kama mutanen ne sakamakon wani “bincike na tsanaki” bayan kama wani da ake zargi da haura gidan ajiyar abinci a ƙaramar hukumar Ohio/Akpor ta jihar.

Biyu daga cikin mutanen farko da aka kama kofur-kofur ne a rundunar sojin Najeriya da ke aiki a jihar Delta, da kuma jami’i a rundunar tsaro ta Civil Defence mai aiki a Kabba da ke jihar Kogi, in ji ta.

Ta ƙara da cewa daga baya ne suka gano wani babban gungu na masu aikata fashi da kuma karkatar da kayan mutane, ciki har da manyan motoci. A cewarta, rundunar ta ƙwace mota ƙirar Toyota Hilux da gungun mutanen ke amfani da ita.

legit nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp