fidelitybank

An kama matashi da zargin satar Babur a Osun

Date:

Wani matashi dan shekara 25 mai suna Adebowale ya shiga hannun jami’an hukumar Osun Amotekun bisa laifin satar babur.

Babur din, kamar yadda jami’an tsaro suka bayyana mallakar wani gida ne na unguwar Aratumi, a yankin Kelebe Osogbo.

Kwamandan rundunar ‘yan sandan Osun Amotekun, Birgediya Janar Bashir Adewinmbi ya ce jami’an tsaro ne suka kama Adebowale a lokacin da suke sintiri na yau da kullun bayan ya aikata hakan da misalin karfe 1 na safiyar Laraba.

Birgediya Janar Adewinmbi yayin da yake tabbatar da kamun a Osogbo a ranar Laraba, ya bayyana cewa an kama Adewale ne bayan ya saci babur TVS a unguwar Aratumi da ke Unguwar Kelebe a Osogbo.

“A cikin tafiyar da babur ne mutanen Amotekun da ke sintiri na yau da kullun suka gan shi suka kama mai laifin.

“Da aka yi masa tambayoyi, mai laifin ya amsa laifinsa.

“An mika shi ga ‘yan sanda don yi masa tambayoyi da kuma gurfanar da shi.”

Adewinmbi ya kuma gargadi masu aikata laifuka da su kaurace wa Osun.

“Ba ma daukar duk wani abu da ke da alaka da tsaron rayukan mutane da dukiyoyi da wasa. Muna aiki cikin hanzari kan duk wani yanki na bayanai da suka shafi tsaro don tabbatar da ko na gaskiya ne ko a’a.”

“Amotekun a shirye yake ya tona asirin masu aikata laifuka a wuraren da suke buya”. Adewinmbi ya tabbatar.

Ya bukaci mazauna yankin da su bayyana masu aikata laifuka a unguwannin su ga rundunar Amotekun domin dakile aikata laifuka a cikin al’umma.

A baya-bayan nan, babban birnin jihar Osun, Osogbo, ya sha fama da tashe-tashen hankulan da suka shafi laifuka, ci gaban ya kara matsin lamba ga gine-ginen tsaron jihar.

An samu rahoton yin garkuwa da mutane har a Osogbo babban birnin jihar.

vanguardnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mashawarcin gwamnan Kano ya rasu bayan harin ‘yan Daba

Sadiq Gentle, babban mai ba da rahoto na musamman...

An fitar da jerin sunayen Matasan ‘yan wasan da za su lashe kyautar Kopa

Masu shirya kyautar Ballon d’Or, sun fitar da jerin...

An fitar da jerin masu tsaron raga da za su lashe kyautar gwarzon bana

An fitar da sunayen wadanda za a zaba don...

Jonathan ne ya fi cancanci ya rike Najeriya Farfesa Tukur

Farfesa Tukur Muhammad-Baba, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Tuntuba...

Mukarraban gwamnati ba zan lamunci dabi’ar zubar da kima ta ba – Abba

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya gargaɗi masu...

WAEC ta sake bude shafinta don duba jarabawar bana

Hukumar shirya jarabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ta bayyana...

Indonesia za ta gina asibiti dubu biyu ga Falasɗinawa

Indonesia ta sanar da cewa za ta kafa wata...

Lauyan Sowore ya bukaci a sake shi cikin gaggawa

Lauyoyin ffitaccen ɗan gwagwarmayar nan kuma ɗan jarida, Omoyele...

Najeriya da Indiya za su haɗa kai na yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fatauncin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Jihohi 19 da za a yi kwana 9 a na ruwan sama harda Kano – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen za a shafe kwana...

Tinubu ya mika sakon ta’aziyya bisa rasuwar matar MKO Abiola

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa bisa...

Abubuwan da Kwamiti ya gano a wajen Kwamishina mai murabus na Kano

A ranar Litinin ne kwamitin binciken badaƙalar belin Danwawu,...
X whatsapp