fidelitybank

An kama matasan da suka kitsa faɗan Saba a Kano

Date:

Rundunar ‘yan sandan Kano ta sanarda kama wani matashi bisa zargin kitsa rikicin da ya ɓarke tsakanin ’yan daba na Kofar Mata da matasan Zango da ya faru kwanan nan.

Matashin mai suna Kabiru Jamilu mai shekara 21, mazaunin rukunin gidaje na Zango Quarters an kamashi ne Unguwar Kofar Mata kusa da Asibitin kwararru na Murtala Mohammed.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda anan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin jagorantar faɗan da aka yi.

Kiyawa ya ci gaba da cewa, binciken ne ya kai ga kama Umar Garba mai shekara 32, mazaunin Zango, wanda aka same shi da wata doguwar wuƙa mai kaifi.

Tuni dai an miƙa waɗanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

Idan za’a iya tunawa dai rikicin daban da akayi kwanakin baya da ya janyo asarar rayuka da raunata wasu, kuma ya yi sanadin asarar kadarorin jama’a da dama a yankin

www.legit news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp