Hukumar tsaro ta NSCDC, a ranar Juma’a ta kama wasu mutane uku da ake zargi da satar batir masu amfani da hasken rana a jihar Jigawa.
Kakakin hukumar NSCDC, Adamu Shehu, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce jami’an NSCDC da ke garin Gujungu sun kama wadanda ake zargin ne a ranar Juma’a da karfe 2 na dare, kan zargin sata da hada baki da ya saba wa sashi na 286 da 96, wanda hukuncinsa a sashi na 96 da 97.
Shehu ya zargi mutanen ukun Umar Adam Abdullahi, Kabiru M. Musa, da Shafi’u Hamza da satar batura masu amfani da hasken rana a kan hanyar Hadejia, cikin garin Gujungu. Ma’aikatar ayyuka ta jihar Jigawa ce ta sanya fitilun titunan da nufin haskaka garin da kuma samar da tsaro.
Shehu ya ce an kama wadanda ake zargin ne da hannu wajen aikata laifin.
A cewarsa: “An kama su ne da batirin Roy 12V/150Ah mai amfani da hasken rana da kuma na’urar caji da aka cire daga jikin fitilar titin, wanda kudinsa ya kai Naira 320,000.”
Ya ce bincike ya nuna cewa a cikin jimillar fitilun masu amfani da hasken rana guda 130 da ke kan manyan titunan garin, 23 an sace musu batir.
Ya tabbatar da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifin da aka aikata kuma za a gurfanar da su a gaban kotu bayan an kammala bincike.