fidelitybank

An kama Matasa 12 dauke da jabun dala dubu 56,300

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta kama wasu mutane 12 da ke da alaka da wasu kungiyoyin jabu guda biyu da ke gudanar da ayyukansu a jihar.

Wadanda ake zargin, shida ne daga kowace kungiya, an same su da kudi dalar Amurka $56,300 na jabun dalar Amurka da kuma naira 265,000 na jabun kudin Najeriya.

A cewar rundunar ‘yan sandan, dukkanin kungiyoyin biyu sun kware wajen kera takardun jabu na dalar Amurka da kuma Nairar Najeriya.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mahid Abubakar, ya bayyana cewa, an gudanar da kamen ne a wurare daban-daban, da ya shafi kananan hukumomin Bajoga, Funakaye da Dukku na jihar Gombe.

A cewar PPRO, an kama ‘ya’yan daya daga cikin kungiyoyin da wasu jabun daloli 500 na dala 100 da kuma N265,000.

Mahid ya bayyana cewa an yi musu dirar mikiya ne bayan da wani Buba Muhammadu ya yi kokarin siyan kwaya daga hannun wani Muhammad Ismail da ke unguwar Sangaru da ke garin Bajoga da kudin jabu na Naira 1,000, inda ya bayyana cewa kama Muhammadu ya kai ga kama wasu ‘yan kungiyar.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargin na farko da suka hada da Buba Muhammadu mai shekaru 45, Jungudo Muhammadu (53), Adamu Yusuf Mallum (30), Abdulhamid Abdullahi (60), Salihu Abdulhamid (50), da Abubakar Abdullahi (35).

An gudanar da bullar kungiyar ta biyu a kauyen Malala da ke karamar hukumar Dukku.

Mahid ya bayyana na biyun wadanda ake zargin “Haruna Adamu mai shekaru 60,  dan kauyen Tanji dake karamar hukumar Darazo ta jihar Bauchi; Garba Ibrahim, dan shekara 25, Hashidu, karamar hukumar Dukku, Jihar Gombe; Samaila Musa, mai shekara 30, Gombe Abba, karamar hukumar Dukku; Sa’adu Muhammed, mai shekara 23, mai lamba 10 Badarawa Quarters, Jihar Kaduna; Yusuf Abdullahi, dan shekara 30, Gombe Abba, karamar hukumar Dukku; Muhammadu Umaru, mai shekara 26, na karamar hukumar Gombe Abba Dukku”.

Ya ce duk wadanda ake zargin sun amsa laifinsu a cikin ayyukan jabun kuma za su fuskanci shari’a a kan haka.

daily 
post news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp