Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Borno ta ce ta kama wata mata da ake zargin ta shahara wajen sace-sacen waya da wasu mutum 84 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.
Laifukan da ake zargin mutanen sun aikata ƙunshi haɗin baki da fyaɗe da kisan kai da fashi da makami da sata da mallamar muggan makamai da kuma shan tabar wiwi.
Da ake holen mutanen a Maiduguri ranar Alhamis, Kakakin rundunar ƴan sandan ta Borno, ASP Daso Nahum.
Ya ce rundunar ta samu rahoton laifuffuka 49 sun kuma samu waɗanda ake zargi 27 da laifi. Ya ƙara da cewa rundunar tana bincike kan wasu laifuffuka 14 sai wasu 31 da aka gurfanar da su a kotu.
Kakakin ya ce an kama matar ranar 28 ga watan Disamban da ya gabata bayan ayyana ta a matsayin wadda ake neman ruwa a jallo sakamakon sace-sacen wayoyin jama’a.
“Yayin bincike, ta faɗi wanda suke satar tare, suna zuwa gidajen mutane a matsayin ƴan aiki inda suke kwashe wayoyin mutanen da suke yi wa aiki.”
“An gano waya kirar Techno LC6 yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike domin kama mutanen da wayar ke hannunsu daga bisani kuma a gurfanar da su a kotu,” kamar yadda kakakin ƴan sandan ya bayyana.


