fidelitybank

An kama Matar da ake zargi da kashe dan kishiyarta da guba a Kaduna

Date:

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta ce, ta kama da tsare wata mata mai suna Zaliha Shu’aibu bisa zargin kashe ɗan kishiyarta ɗan wata uku da haihuwa da maganin ƙwari.

A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar ta Kaduna, DSP Mansur Hassan ya fitar, al’amarin ya faru ne a ranar 13 ga watan nan na Mayu a gidansu da ke ƙauyen Malari a ƙaramar hukumar Soba.

Sanarwar ta ce shaidu sun ce uwar yaron dai ta fita daga ɗakinta domin shiga banɗaki lokacin da kishiyar tata ta shigar mata ɗaki kuma bayan ta koma ɗakin ne ta ga kishiryar rungume da ɗan nata.

Bayan ta miƙa mata jaririn ne sai uwar ɗan ta fahimci yadda kumfa ke fita daga bakin yaron nata sannan kuma akwai rauni a wuyansa, inda yaron ya kece da kuka.

Bayan bincike, rundunar ƴansandan ta ce matar ta tabbatar da cewa ta aikata laifin ne da taimakon ƙanen mijinta wanda shi shi ne ya bata gubar da ta yi amfani a kan jaririn. Ƙanen mijin dai ya gudu ba a kai ga kama shi ba tukunna.

assu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...
X whatsapp