Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, sun cafke wasu mata biyu, bisa zargin satar wani jariri dan mako daya a jihar Ogun.
Rahotanni sun ce, jami’an ‘yan sandan sun kama matan ne a ranar 25 ga watan Yuli, bayan da aka ga daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Chinyere Nwozu ‘yar shekaru 53 tare da jaririyar da misalin karfe 9 na safe a wannan rana, kuma hakan ya haifar da shakku a tsakanin mazauna garin, saboda ta kasa shayar da yaro nono.
Nan take mazauna yankin suka kai rahoton lamarin zuwa shelkwatar sashin Sango Ota kuma an tura wasu jami’an bincike don kama Nwozu.
A yayin da ake yi mata tambayoyi, ta ce, ta sayi yaron ne a hannun wata Ngozi Akaeme da ke zaune a unguwar Agege a jihar Legas kan kudi Naira 500,000.
Karanta wannan: Ana zargin Matashi da satar Lasifikar Massalaci da Janerata
Kakakin rundunar ‘yan sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi ya ce, “Da samun wannan labarin, DPO na Sango Ota, SP Dahiru Saleh, ya yi karin bayani ga jami’an bincikensa zuwa wurin da aka kama matar.”
Bayan kama Akaeme, ta bayyana cewa “ta yi shawarwari da mahaifiyar jaririn da ta amince ta sayar da jaririn.”
A cewar kakakin na jihar Ogun, sun kasa gano mahaifiyar yaron.
Oyeyemi ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sanda, CP Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a mika wadanda ake zargin zuwa hukumar CIID ta jihar, domin ci gaba da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.