fidelitybank

An kama masu zanga-zanga 9 a Borno sakamakon rike tutar Rasha

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ta tabbatar da cafke wasu masu zanga-zanga 9 bisa zargin nuna tutar kasar Rasha a Maiduguri.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yusuf Lawal ne ya bayyana haka yayin da yake bayar da rahoton halin da ake ciki a ranar Talata a Maiduguri, babban birnin jihar.

Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Zannari Tamsu da ke unguwar Gwange, Maiduguri a ranar 5 ga Agusta, 2024.

Lawal ya ce wadanda aka kama sun hada da Khalafi Abdulhamid, Mohammed Abubakar, Mohamed Ibrahim, da Abba Hassan dukkansu mazauna yankin Zannari Tamsu.

“Bugu da kari, an kama wasu masu zanga-zanga biyar a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri, dauke da tutocin kasar Rasha.

“Wadanda ake zargin, Bashir Ahmad, Musa Lawan, Abba Mallam, Habibu Auwal, da Inusa Abdullahi, an mika su zuwa Crack Squad domin gudanar da bincike mai zurfi, tare da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce an kwantar da hankulan muzaharar inda ya ce ‘yan sanda za su ci gaba da sanya ido da kuma sintiri a yankin domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.

nnn news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp