Kakakin ‘yan sandan birnin Dhaka, Faruk Hossain, a ranar Litinin ya bayyana cewa, sama da mutane 500, ciki har da wasu jagororin ‘yan adawa an tsare su, saboda wata zanga-zangar da aka yi a Bangladesh.
Hossain ya ce babban jigo na uku mafi girma a jam’iyyar ta Bangladesh Nationalist Party, BNP, Amir Khosru Mahmud Chowdhury, da mai magana da yawun, Rahul Kabir Rizvi Ahmed na daga cikin wadanda ake tsare da su.
Ya kara da cewa, an kuma kama wani tsohon kyaftin din kwallon kafar kasar ya zama babban jigo a jam’iyyar BNP, Aminul Huq da Mia Golam Parwar, babbar Sakatariyar jam’iyyar Islama ta kasar, Jamaat-e-Islami.
Kakakin ‘yan sandan ya tabbatar da cewa akalla ‘yan sanda uku ne suka mutu a rikicin da ya barke a babban birnin kasar sannan wasu kimanin 1,000 suka jikkata.


