fidelitybank

An kama masu garkuwa da mutane a jihar Taraba har su 20

Date:

Ƴan sanda sun ce sun kama waɗanda ake zargi da yin garkuwa d amutane guda 20 a jihar Taraba.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito cewa hakan ya biyo tattara bayanan sirri da samun korafe-korafe wajen jama’a kan munanan ayyukan masu garkuwan, da suka addabi sassan jihar.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargin a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sandan da ke Jalingo, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Usman, ya bayyana cewa waɗanda ake zargin duk sun amsa aikata laifi.

Ya ce jami’ansu suka ƙwato bindigogi kirar AK-47 guda uku da kuma wata karamar bindiga kirar famfo.

A cewarsa, mutanen da ake zargin sun karɓi sama da naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansa daga iyalan waɗanda suka sace wa ƴan uwa.

“Rundunar ‘yan sandan ba ta ja da baya ba a ƙoƙarinta na ci gaba da farautar ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka a jihar bisa umarnin babban sufeton ‘yan sanda Kayode Egbetokun,” in ji shi.

Usman ya kuma ce rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da farautar ‘yan ta’adda a wasu wuraren da suka fi zafafa ayyukansu, musamman ma a Jalingo, babban birnin jihar.

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp