Hukumar tsaro ta Civil Defence, ta ce, ta kama ganga 150 na man fetur da aka yi safarsa da niyyar fitarwa daga ƙasar tare da kama mutum biyu da ake zargi
Babban kwamandan hukumar mai lura da jihar Akwa Ibom Yusuf Imam ne ya bayyana haka ga manema labarai a Uyo babban birnin jihar ranar Asabar.
Imam ya ce shashen rundunar mai kula da gaɓar teku ne ya yi aiki da bayanan sirrin da ya samu na cewa wasu mutane ɗauke da man fetur a cikin kwale-kwalen katako na kan hanyar zuwa Kamaru.
Ya ƙara da cewa jami’an hukumar sun kuma ƙwace injina biyar tare da wani inji da ake amfani da shi wajen satar mai.
“Jami’an hukumarmu da ke kula da bakin teku sun kama mutum biyu tare da ƙwace gangar man fetur 150 a cikin wani kwale-kwalen katako a cikin teku a daidai yankin ƙaramar hukumar Ibeno ta jihar Akwea Ibom”, kamar yadda babban kwamandan jihar ya bayyana.
Imam ya kuma ƙara jan kunnen masu aikata irin waɗananna laifuka a gabar ruwa – waɗanda ke kawo tarnaki ko yin ƙafar-ungulu ga tattalin arzikin ƙasar – da cewa za su fuskanci mummunan hukunci