Rahotanni na cewa jami’an tsaro a jihar Sokoto, sun kama wani mai safarar makamai ga ƴan Bindiga.
Mutumin mai suna Hamza Suruddubu, ana zargin shi ne da samar wa ƙasurguman ƴanbindigar nan Bello Turji da Boka da kuma Halilu Buzu manyan makaman da suka haɗa da bindigogi da sauran makamai da sauransu.
Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da rundunar sojojin Najeriya kuma ta ce dakarunta sun kashe masu kai hare-hare a faɗin ƙasar har 82 tare da kama 198, kana sun samu nasarar ceto mutum 93 da aka yi garkuwa da su.