Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama wani mutum mai suna Austin Kanu mai shekaru 51 bisa zarginsa da sace wasu yara maza hudu.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin ya fitar a ranar Talata ta ce jami’an rundunar ‘yan sandan yankin Surulere sun kama Kanu.
Wadanda abin ya shafa – Toheeb (16), Isaac (16), Chukwuma (16) da Idowu (18) – an gano su ne a watan Oktoba a wani waje da ke cikin filin wasa na kasa, Surulere.
Babban jami’in tsaro na filin wasan ne ya same su sannan ya sanar da ‘yan sanda.
Hukumar tsaro ta ce binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa Kanu ya lallasa wadanda abin ya shafa daga Ogba da Agege zuwa Surulere.
“Iyayen su da aka tuntube su sun tabbatar da cewa yaran sun bace tun a safiyar ranar 29 ga Oktoba, 2022,” in ji Hundeyin.
Za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken da ake yi.
Kwamishinan ‘yan sanda, Abiodun Alabi ya shawarci mazauna yankin da su yi taka-tsan-tsan tare da kai rahoto ga hukumomin tsaro.