Rundunar jami’an NSCDC reshen jihar Zamfara, ta ce, jami’anta sun kama wani ma’aikacin POS mai suna Mustapha bisa zargin yin hada-hadar kudi a madadin ‘yan bindiga.
Kwamandan jihar, Muhammad Bello Muazu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce an kama mai laifin ne a yayin da yake yin wannan ciniki a yankin Birnin Tsaba da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar.
Ya ce ‘yan sandan sun kwato injinan POS guda biyu, inda ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa wani shugaban ‘yan fashi ne ya saya masa injinan.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya amsa cewa yana amfani da na’urar POS ne kawai wajen yin kasuwanci a madadin ‘yan fashin da yake karewa.
“A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya shaida mana cewa sun buga masa waya daga dajin inda suka umarce shi da ya karbi kudi a madadinsu ya ajiye kudin a wurinsa.” Yace
A cewarsa, idan ‘yan fashi suna son siyan magunguna, man fetur ko kayan abinci, sai su tura wani kai tsaye wurin wanda ake zargin ya karbi kudin ya saya musu duk abin da suke so.
“Daga lura da muka yi, hakan zai shafi yadda ‘yan fashin ke amfani da POS na karkara wajen hada-hadar kasuwanci. Ma’aikatan POS na karkara sun fi kusa da masu aikata laifuka,” ya bayyana