Hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, ta ce, ta kama wani Mahaifi yana rubuta wa dansa jarabawar, a lokacin da ake ci gaba da gudanar da jarrabawar shiga jami’a a fadin kasar nan.
Hukumar ta yi gargadin cewa, ta inganta fasahar bincike na dangwalen dan yatsaya.
Da yake jawabi a Kaduna ranar Laraba, magatakardar hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede wanda ya duba cibiyoyin UTME da ke Kaduna, ya bayyana jin dadinsa kan jarabawar 2024, wanda dalibai miliyan 1.94 a bana ke zana jarabawar.
Ya ce JAMB na bukatar goyon bayan jihohi masu yawan jama’a kamar Legas, domin gina manyan cibiyoyi na CBT irin na Kaduna, wadanda ke daukar mutane 4,000 a kowace rana.
Ya bayyana fatan cewa hukumomi a Legas za su samar da filin da ya dace da JAMB, domin gina cibiyar CBT a birnin.