Hukumar Kwastam ta ce, ta cafke wasu makamai da harsasai a ruwan Legas da ake zargin wasu miyagu sun shigo da su cikin ƙasar ta ɓarauniyar hanya.
Gidan talabijin na Channels ta ruwaito wai jami’in hukumar na cewa sauran abubuwan da aka gano sun haɗa da kakin sojoji, da kuma wasu haramtattun kwayoyi.
Ya ƙara da cewa makaman da aka kwato sun haɗa da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma taharbi ka ruga.
Hukumar ta ce ta samu nasarar kwato kayayyakin ne yayin da ake duba kayayyakin da aka shigo da su cikin ƙasar.
Sai dai babu wasu bayanai na cewa ko an kama wasu ba.
Kamen na zuwa ne watanni takwas bayan da Kwanturola Janar na Hukumar ta Kwastam Adewale Adeniyi, ya shaida wa manema labarai cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da shigo da makamai iri iri 31 ba bisa ka’ida ba a tashar jiragen ruwa na Tin-Can da ke jihar Legas.