Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya ta ce ta kama bakwai daga cikin É—aurarru 16 da suka tsere daga gidan yari na garin Keffi a jihar Nasarawa.
Wata sanarwa da hukumar ta Nigerian Correctional Service ta fitar a jiya Talata ta ce lamarin ya faru da safiyar ranar.
Mai magana da yawun hukumar Umar Abubakar ya ce wasu daga cikin ɗaurarrun ne suka ci ƙarfin gandirobobi, lamarin da ya bai wa mutum 16 damar guduwa nan take.
Hukumar ta kuma ce jamiĘĽanta biyar da ke bakin aiki sun ji raunuka, inda biyu daga cikinsu ke cikin mawuyacin hali kuma suna samun kulawa a wani asibitin gwamnati.
Sai dai sanarwar ta ce an yi nasarar kama mutum bakwai daga cikin ɗaurarrun da suka gudu, kuma babban kwanturolan hukumar, Sylvester Ndidi Nwakuche, ya ƙaddamar da bincike kan lamarin.