fidelitybank

An kama buhun Fulawa 487 marasa kyau a Kano

Date:

Hukumar kare hakkin masu sayayya ta jihar Kano ta kwace kimanin buhun fulawa 487, da ta lalace a wajen ajiyar kaya a kasuwar Dawanau da ke birnin Kano.

Jaridar Punch a Najeriya ta ambato jami’in hulda da jama’a na hukumar Musbahu Yakasai a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, na cewa Daraktan riko na hukuma Dakta Baffa Dan’Agundi ne ya bayyana haka a ofishinsa bayan kwato fulawar.

Dakta Baffa Dan’Agundi ya ce, wasu mutanen kirki ne suka bai wa hukumar tasu bayanan sirri game da fulawar wacce aka kawo kasuwar da nufin sayar da ita. Ya kara da cewa gwajin da aka yi wa samfurin fulawar ya nuna cewa tuni ta dade da lalacewa.

Haka kuma ya ce, hukumar tasu ta kama lemuka masu yawan gaske da suka lalace kuma ake sayar da su a kasuwar Sabon Gari da ke jihar. Gwamnatin jihar Kano ta kwace buhun ‘lalatacciyar’ fulawa 487. In ji BBC.

latest news in nigeria 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp