Rundunar ƴansandan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta kama wani tsoho mai shekara 70 bisa zargin kashe ƙanwarsa saboda rikici kan gado.
Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Lawan Adam Shi’isu ya fitar ya ce tsohon mai suna Adamu Yakubu – ɗan asalin ƙauyen Galadanchi a yankin ƙaramar hukumar Dutse – ya samu saɓani da ƙanwarsa mai suna Hannatu Hashimu, mai shekara 45, kan rabon gadon wata gona da suka gada.
Bayanan binciken farko da ƴansanda suka fitar, ya nuna cewa wanda ake zargin ya jefi ƙanwar tasa da sanda ne a lokacin da gardama ta yi zafi tsakaninsu kan rabon gadon.
Gardamar – wadda ta fara da musayar kalamai – ta munana zuwa rikicin da ya kai ga bai wa hamata iska, inda wanda ake zargin ta kai wa ƙanwar tasa duka da sanda, kamar yadda bayanan ƴansanda suka nuna.
”Marigayiyar ta fita daga gidan a fusace, ta koma gidan aurenta, da zuwanta kuma ta faɗi ta suma, nan take aka garzaya da ita asibiti inda likitocin Babban Asibitin Dutse suka tabbatar da mutuwarta”, in ƴansandan.
Tuni ƴansandan suka kama wanda ake zargin, inda yanzu haka suke gudanar da bincike.