fidelitybank

An kama Ƴan Canji 19 a Kano

Date:

Rundunar ƴan sandan Kano, ta kai wani samame kan kasuwar ƴan canji ta Wapa inda ta kama mutum 29 da ake zargi da gudanar da hada-hadar musayar kuɗin waje ba bisa ƙa’ida ba.

Kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Fesbuk.

Sanarwar ta ce rundunar ta kai samamen ne tare da haɗin gwiwar jami’ai daga hukumar tsaro ta farin kaya DSS.

A cewar kakakin, mutum 12 cikin mutanen da aka kama daga bisa an sake su bayan da aka gaza gano hujjar da ta tabbatar suna gudanar da hada-hadar ba bisa ƙa’ida ba sai kuma ragowar 17 da aka gano kuɗin CFA kimanin dubu 68 sai kuɗin Rupees 30.

Ƙarin binciken da aka yi ya nuna mutanen 17 da ake zargi suna aiki ne ƙarƙashin wani kamfanin ƴan canji da ba shi da rajista kuma za a gurfanar da su gaban kotu.

Rundunar ta ce tana kai samamen ne domin murƙushe masu hada-hadar canjin kuɗi ba bisa ƙa’ida ba da nufin tsaftace kasuwar musayar kuɗi a Najeriya sannan rangadin bai shafi ƴan canjin da ke gudanar da ayyukansu bisa tsarin doka.

leadership news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp