Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan Kwamishinan Zabe na Jihar Kogi.
Hukumar, a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na X a ranar Juma’a, ta ce ‘yan bindigar sun kai hari gidan da karfe 3:30 na safiyar ranar Juma’a.
Ya ce ‘yan bindigar sun yi arangama da jami’an tsaron sama da mintuna 30 har sai da jami’an tsaro suka iso.
Ya kara da cewa ba a samu asarar rai ba yayin harin.
“Da sanyin safiyar yau Juma’a 1 ga watan Disamba, 2023, da misalin karfe 3:30 na safe, wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan kwamishinan zabe (REC) da ke Lokoja, jihar Kogi.
“Yayin da ba a yi asarar rayuka ba, an lalata dukiyoyi a rikicin da ya biyo baya. An tura tawagar jami’an tsaro hadin gwiwa don kare gidan. Wannan lamari dai ya faru ne kwana guda bayan da wasu gungun jama’a suka yiwa ofishin jahar mu kawanya.
“Muna kira da a gudanar da cikakken bincike tare da inganta tsaro ga ma’aikatanmu da kadarorinmu a jihar Kogi,” in ji INEC.


