Ƙungiyar kare ƴan jarida ta duniya ta ‘Reporters Without Borders’ ta ce kimanin ƴan jarida 20 ne aka kai wa hari cikin shekarar 2023 a Najeriya.
Hakan na ƙunshe ne a wani rahoto da ƙungiyar ta fitar a daidai lokacin da ake bikin kare hakkin ƴan jarida ta duniya.
Rahoton ya ce siyasa ta taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da cusguna wa ƴan jarida a nahiyar Afirka, musamman a ƙasashe irin Najeriya, inda aka gudanar da zaɓen shugaban a shekarar ta 2023.
A yanzu haka Najeriya ce ta 112 a jerin ƙasashen duniya kan batun ƴancin ƴan jarida.
Haka nan rahoton ya ce a lokacin zaɓen na Najeriya ƴan siyasa sun yi ƙoƙarin amfani da damarsu wajen murƙushe kafafen yaɗa labaru, yayin da wasu ƴan siyasar kuma suka kafa nasu gidajen yaɗa labarun domin yaɗa fargfaganda.