fidelitybank

An kai samame gidan shugabar kasar Peru sakamakon sanya agogunan gwala-gwalai

Date:

‘Yansanda a Peru sun kai samame gidan shugabar ƙasar Dina Boluart a wani bangare na yaƙin da rashawa, inda suke neman agogunan gwal na Rolex da take sawa.

Hukumomin na neman agoguna sama da 10 da ake ganin Shugaba Dina na sawa a wuraren taruka kuma ake zargin ba ta bayyana su ba a baya.

Binciken ya fara ne lokacin da wani rahoto ya yi magana kan irin agogunan alfarma da take sawa, tun bayan da ta kama aiki a watan Disambar 2022.

Ms Boluart ta ce tsofaffin kadarorinta ne agogunan da ta saya da kumin aikinta.

Tun a farkon wannan watan gwamnati ta sanar da za ta sake bibiyar kadarorinta da ta bayyana na shekaru biyu da suka gabata.

A makon jiya shugabar ta jaddada cewa ta shiga gwamnati da kyakkyawar zuciya kuma tana fatan fita hakan.

Samamen da aka kai da safiyar ranar Asabar, na hadin gwiwa ne tsakanin ‘yansanda da ofishin masu shigar da ƙara kuma an riƙa yada shi a gidan talabijin na ƙasar Latina.

An ga jami’an tsaro a ƙofar gidanta da ke Lima babban birnin ƙasar yayin da wasu kuma suke yunkurin balle mata kofa.

Dalilin wannan aiki an tare duk wani titi da ke zuwa ta wajen ƙofar gidan shugabar.

Samamen na zuwa ne bayan masu shigar da ƙara sunki amincewa da buƙatarta na neman ƙarin lokaci domin gabatar da shaidunta na mallakar agogunan. In ji BBC.

vanguard 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp