fidelitybank

An kai ni Birtaniya na yi aikatau amma na zama fitacce – Sir Mo farah

Date:

An shigar da Sir Mo Farah Birtaniya ne ba bisa ƙa’ida ba a lokacin da yake yaro aka tilasta masa yin aikatau a wani gida.

Fitaccen ɗan tseren Olympics din ya shaida wa BBC cewa waɗanda suka sace shi daga ƙasar Djibouti ne suka sanya masa suna Mohamed Farah.

Sunansa na ainihi Abdi Kahin. Yana da shekara tara a lokacin da wata mata da bai taɓa sani ba ta fitar da shi daga ƙasarsa ta gabashin Afrika. Sai ta kai shi aiki wani waje don ya dinga kula da ƴaƴan gidan, kamar yadda ya faɗa.

Ɗan tseren na tawagar Birtaniya ya ce “na yi ta ƙoƙarin dakatar da hakan, amma na kasa.”

A baya dai ɗan tseren ya taɓa cewa shi da iyayensa ƴan gudun hijirar Somaliya ne da suka tafi Birtaniya.

Amma a wani shiri na BBC da kamfanin Red Bull Studios da BBC News ta ganida aka yaɗa a ranar Laraba, ya ce iyayensa ba su taɓa zuwa Birtaniya ba.

Mahaifiyarsa da ƴan uwansa biyu na zaune ne a wata jiha a yankin Somaliland da ya ɓalle.

Mahaifinsa kuwa ya rasu ne sanadin harbinsa da aka yi tun Sir Mo yana ɗan shekara huɗu a duniya a wani rikici da aka yi a Somaliya.

A shekarar 1991 ne ƙasar Somaliland ta ayyana samun ƴancin kai, amma ƙasashjen duniya ba su yarda da ita ba.

Sir Mo ya ce, yana ɗan shekara takwas zuwa tara aka ɗauke shi daga gida zuwa wajen wani iyali a Djibouti.

Daga can sai wata mata da bai taɓa saninta ba kuma ba shi da alaƙa da ita ta ɗauke shi zuwa Birtaniya.

Ta ce, masa za a kai shi Turai ne, domin ya zauna a wajen wasu dangi – lamarin da ya yi matuƙar faranta masa rai, in ji shi.

“Ban taɓa hawa jirgi ba,” ya ce. Matar ta ce masa ya ce sunansa Mohamed.

Ya ce an ba shi takardun bogi na tafiya da ke ɗauke da hotonsa da sunan “Mohamed Farah” a gefe.

nigeria newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp