Shugaban hukumar zaben ta kasa INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya ce, tun daga shekara ta 2019 zuwa yanzu an kai hari kan ofisoshin hukumar sau 50 a jihohi 15 na kasar.
Ya bayyana haka ne a yau Juma’a lokacin da yake bayani ga kwamitin majalisar wakilan Najeriya da ke bincike a kan barnar da aka yi wa INEC.
A cewar Farfesa Yakubu an kai hari sau takwas a shekara ta 2019 a ofisoshin INEC, sau 22 a 2020, sau 12 a 2021 sannan kuma a 2022 an kai hari sau takwas.
Shugaban INEC din ya ce an fi kai hare-hare kan ofisoshin hukumar a jihar Imo inda aka kai sau 11 sannan kuma sai jihar Osun inda aka kai hari sau bakwai.
Galibin hare-haren an kaddamar da su ne a jihohin da ke kudancin Najeriya.
Farfesa Yakubu ya ce duk da irin wadannan matsalolin, suna ci gaba da gudanar da shirye-shiryen da suka kamata domin tsara zabe mai inganci a Najeriya.