An kai wani hari birnin Auckland na kasar New Zealand, sa’o’i gabani fara gasar Kofin Duniya ta Mata a birnin.
Harin da wani ɗan bindiga ya kai ya raunata mutum shida, ciki har da ‘yan sanda.
Daga baya shi ma maharain ya mutu a wani waje da ake gini a tsakiyar birnin.
Firaministan kasar Chris Hipkins ya ce, harin bai yi kama da na ta’addanci ba, ya kuma tabbatar da cewa, za a ci gaba da gasar Kofin Duniyar ta Mata kamar yadda aka tsara ta.
Tuni dai aka take wasan tsakanin mai masaukin baki New Zealand da kasar Norway.
Yayin da babu wani da ko wata kungiya da ta ɗauki alhakin harin, firaministan kasar ya ce ‘yan sanda sun tabbatar wa al’umma cewa babu wani sauran barazana.
Magajin garin birnin Auckland Wayne Brown ya ce harin ba shi da alaƙa da gasar Kofin Duniya ta Mata da ƙasar ke ɗaukar baƙunci. In ji BBC.