fidelitybank

An kai hari kan ma’aikatan INEC a Anambra

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, ta tabbatar da cewa an kai hari kan ma’aikatan hukumar zabe mai zaman kanta, INEC da wasu ma’aikatan.

Tochukwu Ikenga, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Anambra a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ya ce ma’aikatan INEC na samun horo lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Ma’aikatan INEC tare da wasu jami’an hukumar zabe, daliban jami’a da kAnuma wasu jami’an MDA kan shirin horas da ma’aikatan Adhoc a babban zaben 2023 da ke tafe, ‘yan bindiga sun tarwatsa su.

“Babu wani rai da aka rasa, yayin da rundunar hadin guiwar jami’an tsaro suka yi nasarar ceto tare da hana ‘yan bindiga cutar da jami’an zabe a wani aiki a makarantar sakandare ta Ukpor, karamar hukumar Nnewi ta Kudu.

“An tsaurara matakan tsaro na hadin gwiwa a yankin kuma ana ci gaba da kokarin zakulo masu aikata laifuka.”

Ikenga ya tabbatar wa jama’a dabarun aikin ‘yan sanda da Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Anambra, Echeng Echeng ya dauka na da karfi da kuzari kuma za su iya magance duk wata matsala ta gaggawa da tsaro, kuma za ta tabbatar da zaben 2023 ba tare da tangarda ba a jihar.

current eggon news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp