An kai wa jirgin kwashe mutanen Turkiyya hari a Khartoum, babban birnin Sudan, a cewar ma’aikatar tsaron Turkiyya.
Sai dai babu wanda ya jikkata kuma jirgin ya samu sauka ba tare da wata matsala ba a filin jirgin sojin sama na Wadi Seidna, inda daba bisani aka duba lafiyar jirgin.
Sojojin Sudan sun ɗora laifin harin da aka kai wa jirgin kan dakarun RSF.
Sai dai dakarun RSF sun musanta zargin tare da cewa za ta mutunta yarjejeniyar tsawaita buɗe wuta da aka cimma.
A jiya Alhamis ne ɓangarorin soji da ke faɗa da juna a Sudan suka amince da tsawaita daatar da buɗe wuta a Sudan da ƙarin kwanaki uku.