An kai harin jirgi mara matuki kan gidan Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Caesarea, da ke arewacin Isra’ila, a cewar mai magana da yawunsa.
Netanyahu ba ya cikin gidan lokacin da aka kai harin babu kuma wanda ya jikkata, in ji kakakin nasa.
Tun da farko, sojojin Isra’ila sun ce an kai harin jirage mara matuki guda uku zuwa garin a safiyar yau Asabar.
Ta ce ɗaya daga cikin jiragen ya lalata wani gini, yayin da aka kakkaɓe guda biyu.