fidelitybank

An kafa kwamitin da zai duba sabon mafi karancin albashi

Date:

Kwamitin da gwamnatin tarayya ta kafa kan sabon mafi ƙarancin albashi a ƙasar zai sake zama a mako mai zuwa domin ci gaba da tattauna batun mafi ƙarancin albashin ma’aikatan ƙasar, bayan da ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar suka fice daga tattaunawar ranar Larabar da ta gabata 15 ga watan Mayu.

Cikin wasiƙar gayyatar da shugaban kwamitin, Bukar Goni, ya aike wa mambobin kwamitin a matakan jihohi ya ce kwamitin ya amince da sauya matsayarsa kan naira 48,000 da ya ɗauka ranar Larabar.

Wasiƙar ta yi kira ga shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar, da su gayyaci mambobinsu domin halartar zaman da za a yi ranar Talata 21 ga watan Mayu.

Tun da farko dai ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar sun buƙaci gwamnatin ƙasar ta amince da naira 615,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar, lamarin da ya sa tunaninsu da na kwamitin ya yi hannun riga.

A nasu ɓangare, kamfanoni masu zaman kansu sun amince naira 54,000 a matsayin mafi ƙarancin albashin.

Ƙungiyoyin ƙwadagon dai sun ce sun fice daga tattaunawar ta ranar Laraba ne saboda sun fahimci cewa gwamnatin ƙasar ba da gaske ta yi ba.

www.legit.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp