Gwamnatin jihar Sokoto, ta kafa wani kwamiti da zai bincike batun mallakar filaye da yadda aka sayar da ko a ka yi gwanjon kadadrorin gwamnati a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar Sanata Aminu waziri Tambuwal.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Abubakar Bawa ya fitar, ya ce kwamitin mai mutane biyar ƙarƙashin jagorancin Justice M.A. Pindiga, zai kuma duba asusun gwamnatin jihar domin gano adadin kuɗaɗen da aka samu sakamakon sayar da kadarorin.
Sanarwar ta kara da cewa, kwamitin zai kuma duba batun filayen da sabuwar gwamnatin ta ke zargin gwamnatin da ta shuɗen ta rabar ciki har da gidajen gwamnatin jihar da aka yi yi gwanjonsu.
Haka kuma akwai batun motocin gwamnatin jihar da na kananan hukumomi.
Sauran mambobin kwamitin sun haɗar da Barrister Nasiru Muhammed Binji a matsayin sakatare, sai Chief Jacob E. Ochidi, SAN, da Alhaji Usman Abubakar da kuma Barrister Lema Sambo Wali a matsayin mambobi.
An bai wa kwamitin watanni biyu domin gabatar da rahoton sakamkon bicikensa.