Shugaban kamfanin Twitter ya kaddamar da sabon tambarin dandalin sada zumuntar, mai dauke da harafin X, wanda zai maye gurbin shuÉ—in tsuntsu da ake amfani da shi a baya.
A cikin wata sanarwa da twitter ya wallafa a safiyar Litinin, babbar jami’ar kamfanin, Linda Yaccarino ta ce “X ya bayyana!”
Haka zalika Musk ya ce za a daina kiran sakonnin da aka wallafa a twitter da “Tweets” sai dai a riÆ™a cewa “x’s”.
Hamshakin attajirin ya canza hoton shafinsa zuwa sabon tambarin na twitter.
A ranar Lahadin da ta gabata ne attajirin ya ce yana shirin canza tambarin Twitter, yana mai cewa: “Kuma nan ba da jimawa ba za mu yi bankwana da tambarin twitter na tsutsu da aka saba amfani da shi”