fidelitybank

An kaddamar da bincike kan lugudan wuta a Katsina da sojoji su ka yi

Date:

Rundunar tsaron sojin saman Najeriya, ta ce za ta yi bincike kan zargin cewa jirgin yaƙin soji ya kashe mutum shida bisa ‘kuskure’ a lokacin da sojojin ke bin wani gungun ƴan bindiga a jihar Katsina.

A cikin wata sanarwa da daraktan sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na shelkwatar rundunar, Air Vice Marshal Olusola F Akinboyewa ya fitar, ya ce Rundunar ta yi matuƙar damuwa da rahotannin, kuma babban hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Hassan Abubakar ya bayar da umurnin gudanar da cikkaken bincike da kuma ɗaukar matakan da suka dace.

A ƙarshen mako ne rahotanni daga jihar Katsina, mai fama da matsalar ƴan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya, suka bayyana cewa wani jirgin sojin saman Najeriya ya kai hari kan fararen hula, lamarin da ya haifar da asarar rayuka.

Sojojin Najeriya sun yi ƙaurin suna wajen kai harin kuskure kan fararen hula a ƴakin da suke yi da matsalar tsaro a yankunan Najeriya.

Sai dai a cikin sanarwar da ta fitar a yau Litinin, rundunar ta ce sojojin sama da ke aiki ƙarakshin dakarun Fansar Yamma sun yi nasara a harin da suka kai a tsaunin Yauni a gundumar Zakka da ke karamar hukumar Safana a jihar Katsina inda suka yi nasarar kashe ƴan bindiga da dama kuma suka taimaka wajen daƙile harin da aka kai wa ƴansanda da kuma ƴan sinitirin jihar Katsina.

Ya kuma ce sun kai harin ne bayan samun sahihan bayanai da ke nuna cewa an kai wa yankin da ƴansandan suke hari inda aka kashe jami’ai biyu da ƴan sintiri huɗu, kuma an samu tabbacin cewa ƴan bindigar na boye a tsaunin Yauni da ke kusa da yankin kafin kai harin.

legit nigeria news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp