Rundunar sojin Isra’ila ta ce, an jikkata sojojin ta dama sakamakon harin makami mai linzami da aka harba daga Lebanon.
Ta ce harin ya lalata aya daga cikin motocinta da ke yankin Beit Hillel a arewacin Isra’ila, ‘yan kilomitoci daga iyakarta da Lebanon.
sai dai ba ta fai adadin sojojin da aka raunata ba da kuma wanda ya kai musu harin.
Rundunar ta ce tana kai wa yankin da makaman suka fito hare-hare da makaman atilare.


