Yayin da ake ci gaba da bayyana sakamakon zaɓen gwamna da aka kammala a jihar Adamawa, an jibge jami’an tsaro a wurin da ake bayyana sakamakon zaben a Yola, babban birnin jihar.
A cibiyar ce ake sa ran sanar da sakamakon zaɓen a yau Lahadi.
An ɗage bayyana sakamkon zaɓen da daddare a ranar Asabar, inda babban jami’in bayyana sakamakon zaɓe na jihar ya sanar cewa za a ci gaba da ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi.
Al’ummar jihar dai na nan suna dakon sakamakon, kamar sauran al’ummun wasu jihohin da aka gudanar da zaɓen na ranar Asabar 15, ga watan Afurilu.
An gudanar da zaɓen ne a rumfunan zaɓe 67, inda aka kasa kammala zaɓe na ranar 18 ga watan Maris, wanda a sanadiyyar haka ne INEC ta ce zaɓen bai kammala ba


