Mazauna Lokoja babban birnin jihar koji na cikin halin zaman dar-dar, bayan da aka ji karar wani abun fashewa da safiyar ranar Talata.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa an samu fashewar ne a kusa da harabar ofishin Sakataren gwamnatin jihar, wanda ke kusa da ma’aikatar harkokin mata ta jihar.
Fashewar ta auku ne da misalin karfe 8:00 na safe a daidai lokacin da ma’aikata da ‘yan kasuwa ke kokarin fita zuwa wuraren harkokinsu.
Kwamshinan ‘yan sanda na jihar Edward Egbuka ya tabbatar da aukuwar lamarin.