fidelitybank

An jefi shugaban kasar Kenya da Takalma

Date:

Gwamnatin Kenya ta bayyana jifa da takalmi da aka yi wa shugaban ƙasar, William Ruto a wani gangamin siyasa a ranar Lahadi, a matsayin “abun kunya”.

Bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda takalmin ya bugi hannun shugaban ƙasar na hagu, a yayin da ya ke magana.

Mai magana da yawun gwamnatin ƙasar, Isaac Mwaura, ya yi Alla-wadai da lamarin tare da kiran a kama waɗanda suka aikata hakan.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ya ce “me zai faru idan dukkanmu muka fara jifar juna da takalma? Wane tarbiyya muke koya wa ƴaƴan mu?” Ya kuma buƙaci a girmama muƙamin shugaban ƙasa.

Kafofin watsa labarai a Kenya na bayar da rahoton cewa an kama mutum uku dangane da lamarin, sai dai ƴan sanda ba su tabbatar da hakan ba.

Wasu ‘yan majalisar ƙasar sun kuma soki wannan lamari inda suke kallonsa a matsayin babban giɓi a tsaro.

nigeria news.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Yunwa na kara tsananta a arewa maso gabashin Najeriya – ICRC

Kungiyar agaji ta Red cross (ICRC) ta bayyana yadda...

Ba zan taba watsawa Tinubu kasa a ido ba – IBB

Ɗan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wato...

Natasha kar ki kuskura ki dawo aiki – Majalisa

Majalisar Dattijai ta buƙaci Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta dakatar...

Za a yi ruwan sama da iska mai ƙarfi a jihohi harda Kano – NiMET

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMET) ta fitar...

Obi da El-Rufa’i za su koma jam’iyyar mu a hukumance – ADC

Sakataren yada labarai na rikon kwarya na jam’iyyar African...

Za mu tattauna da tarayyar Turai a kan Nukiliyarmu – Iran

Iran ta tabbatar cewa za ta gudanar da tattaunawa...

Mu na gargadin Isra’ila kan korar al’ummar Gaza daga yankin su – MDD

Hukumar kula da ayyukan jin-ƙai ta Majalisar Ɗinkin Duniya...

Rikici ya kuma balle a Syria

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan'adam sun ce, wani sabon rikici...

Tsofaffin ‘Yansanda na da ‘yancin yin zanga-zanga – A Cewar Amnesty

Ƙungiyar Amnesty International ta ce tsofaffin ƴansandan Najeriya girmamawa...

Buhari ya yi wa Najeriya hidimar da ba za a manta da shi ba – António Guterres

Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) António Guterres...

Binani ta koma jam’iyyar haɗaka ta ADC

'Yartakarar gwamnan jihar Adamawa a zaɓen 2023, Sanata Aishatu...

A Talata zan koma aiki na a majalisa – Natasha

Yar majalisar Dattawa, Sanata Natasha Akpoti, ta ci alwashin...
X whatsapp