fidelitybank

An harbi magoyin bayan Arsenal yayin murnar cin Man Utd

Date:

Ana zargin cewa wani jami’in tsaro ya harbe wani magoyin bayan Arsenal a Uganda, lokacin da yake murnar nasarar da ƙungiyarsa ta samu kan Manchester United a gasar Firimiyar Ingila ranar Laraba.

An kuma jikkata wani yayin da jami’in tsaron ya buɗe wuta kan dandazon muagoya bayan Arsenal da ke murna a wani wajen cin abinci a garin Lukaya, mai nisan kilomita 100 da Kampala babban birnin ƙasar.

Lamarin ya faru ne ana daf da kammala buga wasan, wanda Arsenal ta samu nasara da 2-0.

Wani ɗan jarida a yankin ya faɗa wa BBC cewa mai kula da wajen da ake kallon wasan ya fusata da irin hayaniyar da magoyan Arsenal ɗin ke yi, inda ya buƙaci jami’in tsaron da ya ɗauki mataki.

Sai dai mutanen ba su saduda ba, inda suka ci gaba da murna da sowa.

Wani shaida ya faɗa wa ɗan jaridar cewa, mai wajen cin abincin da kuma ake kallon wasan ya kashe injin da ke bayar da hasken wuta a wajen, abin da ya fusata masu kallon har ta kai suka ƙara ihu fiye da farko.

A lokacin ne kuma ake zargin mai gadin wurin ya buɗe musu wuta.

An ruwaito cewa wanda lamarin ya rutsa da shi John Ssenyonga, mai shekara 30, ya mutu nan take a wajen.

An kuma garzaya da wani magoyin bayan Arsenal ɗin Lawrence Mugejera zuwa asibiti bayan samun raunuka.

Mai gadin da kuma manajan da ke kula da wurin sun tsere bayan faruwar lamarin, inda jamin’an tsaron ke ci gaba da farautarsu.

mmm.nnn.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp