fidelitybank

An harbe ‘yan bindiga biyu tare da kubutar da wani a Katsina

Date:

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina a ranar Laraba, ta ce, jami’anta sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da kubutar da wani da aka yi garkuwa da su.

‘Yan sandan sun kuma fatattaki ‘yan bindiga da dama a wasu kauyuka biyu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, SP Gambo Isah, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa ne a ranar 12 ga watan Fabrairun 2023, da misalin karfe 04:45, inda ‘yan ta’addan suka kai farmaki a kauyen Kitibawa. Karamar hukumar Dutsinma tare da yin garkuwa da wani Alhaji Ado Rumawa.

Karanta Wannan: Buhari ya yi Allah wadai da harin jihar Katsina

Ya ce nan take kwamandan yankin na Dutsinma ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da ke sintiri zuwa yankin, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan, inda ya ce rundunar ta samu nasarar fatattakar ‘yan ta’addan inda aka kashe daya daga cikinsu.

A cewarsa, an kubutar da wani da aka yi garkuwa da shi ba tare da jin rauni ba yayin da da yawa daga cikin ‘yan ta’addan suka gudu da raunukan harbin bindiga.

Ya yi bayanin cewa jami’ai da mazaje na kan hanyarsu ta zuwa wurin, domin kamo sauran ‘yan bindigar da suka jikkata

“An kashe wani dan ta’adda a hanyar Danja zuwa Bakori, “a daidai wannan rana da misalin karfe 01:35, an samu kiran gaggawa cewa wasu ‘yan ta’adda kimanin 20 dauke da muggan makamai sun tare hanyar Danja zuwa Bakori, suna fashin fasinjojin da ba su ji ba ba su gani ba. Unguwan Balarabe junction.

“Rundunar ta Danja ta jagoranci tawagar ‘yan sanda zuwa yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar.”

latest news in lokoja, kogi state

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp