Wasu ‘yan bindiga sun harbe wasu sojoji biyu a wani sansanin soji da ke Tegina a karamar hukumar Rafi a jihar Neja, a wani artabu da suka yi da safiyar ranar Litinin.
An bayar da rahoton cewa an kashe wani da ake zargin shugaban ‘yan fashi ne a rikicin.
Tun da farko ‘yan bindigar sun nufi kananan hukumomin Mashegu da Wushishi domin yin awon gaba da shanu a yankunan, amma sun yanke shawarar kai hari a sansanin sojoji, lamarin da ya kai ga musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Rafi, Alhaji Ayuba Usman Katako, ya bayyana cewa jami’an soji biyu da aka harba a yayin artabu da bindiga suna karbar magani a asibitin kwararru na IBB dake Minna.
Sai dai ya bayyana cewa an kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan da ake zargin shugabansu ne yayin da yake nuna rashin jin dadin yadda ake ci gaba da kai hare-haren ba-zato kan jami’an tsaro a jihar.
Ayuba Katako ya bayyana cewa: “Sojoji da ‘yan sanda da ’yan banga suna bakin kokarinsu a jihar don tabbatar da zaman lafiya da tsaro na rayuka da dukiyoyi, don haka ya cancanci a yaba wa ‘yan Najeriya.”
Daga nan sai ya yi kira da a kara hakuri da goyon baya da addu’o’in jama’a domin shawo kan kalubalen tsaro da ke addabar jihar da Najeriya baki daya.
Sai dai kokarin da ake na jin martanin sojoji a jihar ya ci tura a lokacin da ake gabatar da wannan rahoto.