Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ribas, sun kashe akalla mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne bayan wani artabu da maharan.
Lamarin ya afku ne a ranar Juma’a lokacin da jami’an ‘yan sanda suka kai hari a kogon masu garkuwa da mutane a dajin Oyigbo/Igbo-Etche.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Grace Inringe-Koko, ya fitar, ta ce harin ya biyo bayan bayanan sirri da aka samu ga rundunar.
Ta ce wadanda ake zargin sun samu munanan raunuka a yayin artabu da ‘yan bindigar kuma an tabbatar da mutuwarsu a asibitin koyarwa na jami’ar Fatakwal.
A cewar jami’in hulda da jama na rundunar ya ce, ‘yan sandan sun kwato AK47 guda daya da kuma harsasai masu rai guda 18 a samamen da suka dauki sama da awa daya.
Sanarwar ta kara da cewa, “Jami’an tsaron sun yi aiki ne da bayanan sirri da aka tattara akan kungiyar masu garkuwa da mutane. Da ganin tawagar ‘yan sandan sai ‘yan bindigar suka bude musu wuta.
“A yayin da aka yi artabu da bindigar da ya dauki kimanin awa daya, shugaban kungiyar, wanda aka bayyana sunansa da Aka Blacky, ya samu rauni sosai.
“Wani wanda ake zargi mai suna Peter Nwafor ‘m’ an harbe shi a lokacin da yake kokarin tserewa.
“An kai mutanen biyu zuwa asibitin koyarwa na Jami’ar Fatakwal inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da mutuwarsu.
“An ajiye gawarwakinsu a dakin ajiye gawa na UPTH.
“Kungiyar tana da alaƙa da sace wata mata da diyarta a ranar 18 ga Maris 2023 tare da Garrison, Fatakwal. Idan dai za a iya tunawa a baya an kama wasu ‘yan kungiyar guda biyu. Abubuwan da aka gano a wurin sun hada da bindiga AK47 guda 1 da kuma harsasai masu rai guda 18”.