A ranar Lahadin da ta gabata ne aka harbe wasu mutane biyu a wani kazamin rikici da ya barke tsakanin wasu da ake zargin ’yan bindiga ne daga yankin Isale Offa da Ojale, a garin Offa da ke karamar hukumar Offa ta jihar Kwara, kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito.
Rikicin mai zubar da jini ya afku ne da misalin karfe 1130.
Kafin isowar ‘yan sandan an kai harin, an harbe biyu daga cikin ‘yan ta’addan mai suna Samad Adeyemi ‘m’ mai shekaru 21 a duniya Isale Offa da kuma wani Abdulahi Mohammed ‘m’ mai shekaru 20 a Ojale.
A cewar jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Mista Okasanmi Ajayi a wata sanarwa a Ilorin ranar Lahadi, “Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.”
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Talata Assayomo, ya shawarci jama’a da su rika sanar da ‘yan sanda bayanai game da munanan ayyuka har ya bayar da lambobin waya kamar haka: 08125275046 da 07032069501.