An harbe Buhari Muhammad dan shekaru 17 a duniya a unguwar Rangyel da ke karamar hukumar Bassa ta jihar Filato. Kazalika an kashe shanu hudu tare da jikkata wasu biyar a lamarin.
Shugaban kungiyar Gan Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (GAFDAN) na jihar, Abdullahi Garba, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya shaida wa Aminiya a ranar Alhamis cewa ’yan sanda sun gano gawar marigayin.
Lamarin na baya-bayan nan ya zo ne sa’o’i kadan bayan an kashe wasu ‘yan kabilar Irigwe biyu a cikin ayarin motocin dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Jos ta Arewa/Bassa, Musa Agah.
Garba ya ce an kai wa Muhammad hari ne a lokacin da ya dauki shanunsa ya yi kiwo, kwatsam ‘yan bindigar suka bude masa wuta.
ASP Ubah Gabriel, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, bai amsa sakon SMS da wakilinmu ya aike masa ba.