Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba da ake zargin ‘yan ta’adda ne, sun kashe Baturan ‘yan sanda reshen Naka, Mahmud Abubakar, a jihar Benue.
Rahotanni sun nuna cewa, maharan sun kai wa Sufeton ‘yan sandan hari ne a ranar Talata a lokacin da yake dawowa daga Makurdi, inda ya je yi wa rakiyar zaman lafiya.
Naka hedikwatar karamar hukumar Gwer ta yamma ce a jihar Benue, inji rahoton Naija News Hausa.
Jaridar PUNCH ta rawaito wata majiya na cewa harin ya faru ne da misalin karfe 3:30 na yammacin jiya. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Binuwai, Wale Abbas, ya shaida wa manema labarai ta wayar tarho cewa an yi wa dan sandan kwanton bauna ne a lokacin da yake komawa ofishinsa.
Ya ce, “Gaskiya ne an kashe DPO; yaje rakiya ne suka share masa hanya. Akan hanyarsa ta zuwa Naka suka yi masa kwanton bauna.”
Karanta Wannan: Baturen ‘yan sanda a Jigawa ya rasu a ofishin sa
An tattaro daga ranar Lahadi zuwa Talata, akalla wasu mutane biyar wasu da ake zargin makiyaya ne suka kashe a wasu al’ummomin da ke majalisar.
A halin da ake ciki, Shugaban karamar hukumar Gwer West, Ayande Andrew, ya yi ikirarin cewa makiyaya ne suka kashe DPO.
Ya ce, “Makiyaya ne suka tare hanyar kuma DPO na kan hanyarsa ta zuwa Makurdi ne suka yi masa kwanton bauna; shi kadai ne a cikin motar da ke kan hanyar.”
A kan sauran biyar da aka kashe, ya ce, “Makiyaya sun kashe wani a safiyar yau (Talata) a kauyen Tsenge, sannan kuma an kashe wasu mutane hudu a unguwar Babowa ranar Lahadi.”