An harbe ɗan takarar shugaban ƙasa a wurin gangamin neman zaɓe a birnin Quito na Equador.
Hotunan intanet sun nuna lokacin da Fernando Villavi-cencio ke ƙoƙarin shiga mota sai maharan suka buɗe masa wuta. Tuni su ma aka kashe su.
Rahotanni sun ce harsasai da dama sun samu Mista Farnando, kuma har yanzu ba a san ko su waye suka aikata kisarn ba, amma dai ana zargin hannun ƙungiyoyi masu safarar ƙwaya da ya sha alwashin ɗaukar matakin daƙile su idan aka zaɓe shi shugaban ƙasar. In ji BBC.
Shugaba Guillermo Lasso ya ce ya kaɗu matuka, ya kuma sha alwashin ɗaukar mataki da tabbatar da ganin hakan bai kawo cikas ga shirin zaɓen shugaban ƙasar da aka shirya yi karshen watan Agusta ba.