A tsawon ranar Asabar , an yi ta harba rokoki masu yawa daga Zirin Gaza zuwa cikin Isra’ila.
Kafofin yaɗa laraban ƙasar sun ce wasu daga ciki sun faɗa ƙasar, daga ciki har da waɗanda suka faɗa birnin Ashkelon da ke kudancin ƙasar.
Inda wani roka da aka harba ya faɗa da asubahin ranar Asabar, to sai dai babu rahoton jikkata.
A ranar Asabar da rana ne aka girke na’urorin jiniya da ke ankararwa idan an harba rokokin a birnin Tel Aviv da garuruwan da ke kewaye.
Shafin intanet na kafar yaɗa labaran Ynet ta Isra’ila ya ce wani makamin roka da aka harba ya faɗa warin ajiye ƙananan motoci a kiryat Ono da ke wajen birnin tel Aviv, lamarin da ya sa motoci da dama suka tarwatse.
Ynet ya kuma ruwaito cewa wani mutum mai kimanin shekara 50 a Holon ya gigice sanadiyyar hayaƙi, yayin da wasu mutum biyu suka jikkata a birnin Tel Aviv.