Hukumar tsaro ta Isra’ila ta ce, an harba makamai masu linzami zuwa cikin ƙasar daga Lebanon.
Ta ce an harbo makaman ne daga yankin Galilee, amma sun faɗa ne a wani yanki da babu kowa, kuma babu wanda ya jikkata.
A wani saƙo ta shafin X, IDF ta ce dakarunta sun kai hari kan “wuraren tsare mutane na ƴan ta’adda” a Lebanon.
Ana yawan samun artabu tsakanin dakarun Isra’ila da mayaƙa a kan iyakar Isra’ila da Lebanon a kusan kowace rana.
Ana zargin mayaƙan Hezbollah da ke samun goyon bayan Iran da hannu